Za A Sallami Matasa 500,000 Dake Cin Gajiyar Tallafin N-Power, Za A Fara Diban Sabbi Daga Ranar 26 Ga Wannan Watan
https://npower.fmhds.gov.ng/start/application
Za A Sallami Matasa 500,000 Dake Cin Gajiyar Tallafin N-Power, Za A Fara Diban Sabbi Daga Ranar 26 Ga Wannan Watan
Daga Comr Abba Sani Pantami https://npower.fmhds.gov.ng/start/application
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa tana shirin sallamar duka wadanda ke cin gajiyar tallafi na N-Power a kasar nan, da suka kai mutum 500,000 a fadin kasar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Gwamnati ta ce za ta dibi sabbi idan ta sallami wadanda suke cikin shirin yanzu.
Kakakin ma’aikatar jinkai, Rhoda Iliya ta ce wadanda suke rukunin A za su yi sallama da shirin a 30 ga watan Yuni, sai kuma rukunin B za su yi sallama da shirin a karshen watan Yuli.
Bayan wadannan rukuni sun yi sallama da shirin za a dauki sabbin matasa a sabon rukuni na C da za su fara aiki daga 26 ga Yuli.
Gwamnati za ata sanar da sabbin matakai da za a bi wajen shiga shirin da za a fara na sabbin rukunonin A da B nan ba da dadewa ba. Sannan kuma duk wanda ya amfana da shirin a baya ba za a dauke shi a sabbin rukunonin shirin na A da B ba.
Za a bude shafin cika fam daga ranar 26 ga watan Yuni domin daukar sabbin wadanda za su mori shirin. https://npower.fmhds.gov.ng/start/application
Zuwa yanzu muna tsara yadda za'a dauki wasu daga cikin wadanda suka mori shirin a baya ta hanyar koya musu sana’o’i da basu jari, sannna kuma yi wa kamfanoni masu zaman kansu tayin su domin su dauke su aiki. https://npower.fmhds.gov.ng/start/application
Za A Sallami Matasa 500,000 Dake Cin Gajiyar Tallafin N-Power, Za A Fara Diban Sabbi Daga Ranar 26 Ga Wannan Watan
Reviewed by SAMSONGALAXY.com
on
2:00 AM
Rating:
Reviewed by SAMSONGALAXY.com
on
2:00 AM
Rating:


No comments: