Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Yi Bitar Dokar Da Ta Sa Na Kulle

Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Yi Bitar Dokar Da Ta Sa Na Kulle

Jawabin Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ga al’ummar Jihar Kaduna game da bitan dokar kulle

Ya ku al’ummar Jihar Kaduna,
1. A madadin Gwamnatin Jihar Kaduna ina amfani da wannan dama domin in mika godiya ga al’umma na irin jajircewar da suka yi tun daga lokacin da Gwamnati ta sanya dokar kulle a ranar 26 ga watan Maris 2020. Dokar wanda aka sanya na kwana talatin sannan daga bisani aka kara wasu kwanaki talatin a ranar 26 ga watan Afrilu domin dakile yaduwar cutar Covid-19.


2. A cikin wadannan kwanaki sittin da aka yi, al’ummar Jihar Kaduna sun yi kokari matuka na irin hakurin da suka yi game da wannan doka ta killacewa. Mutane da dama daga cikinku sun yi kokari wurin daukan matakan riga-kafi ta hanyar sanya takunkumi da zaman gida da wanke hannaye da sabulu akai-akai da ba da tazara da kaurace wa cinkoson jama’a. Ina rokon ku da ku ci gaba da wannan dabi’a mai kyau domin kare al’ummarmu.


3. Gwamnatin Jihar Kaduna tana mika godiya ga al’umma na yadda suka fahimci cewa duk wadannan matakan riga-kafi da ake dauka ana yi domin kare rayukan al’umma daga kamuwa da wannan annoba ta Covid-19. Wannan hadin-kan da kuka bayar ya taimaka matuka wurin dakile yaduwar wannan cuta.

4. Muna gode muku na goyon bayan da kuke ba mu a kokarin da muke yi na kare rayukanku. Duk wasu matakai da muke dauka muna dauka ne domin kare rayukan al’ummarmu saboda a dakile yaduwar wannan cuta cikin  kankanin lokaci mutanenmu su samu damar komawa su ci gaba da gudanar da harkokin rayuwarsu.


5. Ba za mu taba manta irin goyon bayan da al’ummarmu suke ba mu ba. Duk da cewa muna da mutanen da suka kamu da wannan cuta a wannan jihar, in baicin irin hadin-kan da kuke ba mu da watakila yawan jama’an da suka kamu da wannan cuta ya fi haka yawa.


6. Dole Gwamnati da al’umma su yi aiki tare domin kare rayukan al’umma. Hatsarin da yake tattare da wannan cuta ta COVID-19 ba wai ba shi ba ne yanzu, har yanzu wannan cuta tana nan tana yaduwa kuma tana la’anta rayukan al’umma.


7. Tun lokacin da Gwamnati ta dauki matakin kara tsawaida dokar kulle na kwana talatin, ta nada wani kwamiti na manyan jami’an gwamnati tsara yadda za a yi al’amurra su farfado bayan wucewar wannan annoba. Wannan kwamiti ya mika rahotonsa kuma ya bayar da shawarar yadda za a bude Jihar Kaduna ba tare an jefa rayuka cikin hatsari ba, ciki har da samar da cikakkun bayanai game da harkar lafiya. Wannan kuma abu ne mai matukar muhimmanci lura da yadda cutar ke yaduwa a jiharmu da kuma jihohi makwaftanmu. Mafi yawan wadanda suka kamu da wannan ciwon a Kaduna sun kamu ne ta hanyar wani wanda ya yi tafiya zuwa wata jiha.


8. Bayan kwana sittin da sanya wannan doka, Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi bitan wannan dokar ta kulle kuma Gwamna El-Rufai ya amince da kara wa’adin dokar zaman gida na tsawon mako biyu tare da wasu yin wasu canje canje domin ba wasu fannoni damar budewa. Wadannan matakan ana dauka ne domin kare rayukan al’umma da kuma ba jama’a dama su fita su nemi kudi domin su yi yaki da Covid-19 sannan a hankali kowa ya dawo ya ci gaba da gudanar da harkokin rayuwarsa.


9. Gwamnatin Jihar Kaduna na sane da irin kokarin da al’ummarta suka yi da kuma irin matsalolin da suke fuskanta a kokarin da ake yi na yaki da Covid-19. Wannan sassaucin da Gwamnati ke yi yana bukatar jama’a su jajirce wurin bin dokokin masana kiwon lafiya, musamman abin da ya shafi sanya takunkumi a waje, da bayar da tazara, da wanke hannaye akai-akai da sabulu da ruwa, sannan da kaurace wa tarurruka mai cinkoson jama’a. Jama’a ya kamata su sani kin kiyaye wadannan dokokin na iya sanya gwamnati ta kara tsaurara dokokin nan. Haka kuma kara yaduwar wannan cuta ta Covid-19 na iya sanya gwamnati ta tsaurara wadannan matakan.


10. Wannan makon, sassauci na ranakun fita zai kasance ranar Laraba da Alhamis.


11. Amma kuma daga ranar Litinin 1 ga watan Yuni 2020, wannan sabuwar dokar za ta fara aiki. Wannan sabuwar dokar za ta ba jama’a dama su fita ranar Talata, da Laraba da kuma Alhamis. Za a ci gaba da cin kasuwanni na wucin-gadi daga karfe goma na safe zuwa karfe hudu na yamma, sannan ya kamata jama’a suna iya ci gaba da harkokinsu daga shida na safe zuwa shida na yamma a wadannan ranakun fitan. Sannan manyan kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a rufe kuma an gargadi masu neman su mayar da bakin tituna kasuwanni da su bari.


12. Sannan wannan sabuwar dokar ta bayar da damar sauran masu sana’o’I da su fito su ci gaba da gudanar da harkokinsu a wadannan ranakun amma suna masu bin umurnin likitoci da jami’an kiwon lafiya ciki kuwa har da bayar da tazara. Kamfanoni masu zaman kansu su ma suna da damar budewa a ranakun Talata da Laraba da Alhamis. Wannan sassaucin ya shafi masu sauaran sana’o’i kamarsu walda, faci, kaninkanci da sauran masu sana’o’i makamantansu suk suna iya fitowa a wadannan ranakun.


13. Amma duk da haka, dokar nan da ta hana tafiye-tafiye daga wannan gari zuwa wancan gari na nan. Saboda haka, jami’an gwamnati da kotunan ta-fi-da-gidanka na nan domin sun tabbatar sun hana mutane yada wannan kwayar cutar. Sannan dokar hana fita da daddare nan nan daga karfe shida na yamma zuwa shida na safe.


14. Budu da kari, makarantu da wuraren ibadu da kasuwanni za su ci gaba da kasancewa a kulle. Haka kuma jami’an gwamnati za ta ci gaba da tuntubar malaman addinai da shugabannin al’umma da shugabannin sufuri da na kasuwanni da masu makarantu lokaci zuwa lokaci kan yadda za a bude wadannan wuraren.


15. Sannan an amince a bude wuraren cin abinci amma tare da sharadin sai dai mutum ya siya ya tafi gida ya ci a can. Amma wurare irinsu mashaya da wuraren wasanni da shagulgula za su ci gaba da kasancewa a kulle har da otal otal din da ba a ba su lasisin kasancewa cikin wadanda ake bukatar aikinsu a ko da yaushe.


16. Gwamnatin Jihar Kaduna ta gwada mutum dubu daya da dari tara, a ciki ta samu mutum dari da tamainin da tara wadanda suka kamu da Covid-19. Gwamnati ta so a ce ta yi wannan gwajin fiye da haka amma saboda wasu matsaloli hakan bai yiwu ba. Gwamnati za ta yi kokari a wannan mako biyun da aka kara wurin ganin an kara adadin yawan mutanen da ake yi wa gwajin.


17. Ma’aikatun Gwamnati ma za su yi amfani da wadanann makonni biyun domin fara shirye shiryen dawowa aiki. Shugabannin ma’aikatu da sashe sashe na gwamnati za su tabbatar an yi tsarin bayar da tazara da samar da abubuwan wanke hannu a ofisoshi.  

18. Haka kuma gwamnati za ta ci gaba da tallafa wa masu karamin karfi da gajiyayyu da marasa galihu da tallafin kayan abinci. Yanzu haka ana aikin rabon kayan tallafin abinci kashi na biyu a kananan hukumomi goma sha hudu. Ina tabbatar muku za mu kaddamar da kashi na uku na rabon tallafin abincin nan a kananan hukumominmu ashirin da uku.

19. Zan so in yi amfani da wannan dama domin gode wa manyan jami’an gwamnati na yadda suke taimakawa wurin sanya ido kan dokar nan ta hana tafiye-tafiye kar a shigo mana jiha. Sannan gwamnati na mika godiya ga jami’an tsaro musamman KASTLEA da Hukumar Sintiri ta Jihar Kaduna game da irin namijin kokarin da suke yi.


20. Kamar yadda na ce a baya, hakkin kare jiharmu daga yaduwar Covid-19 ya rataya ne kan daidaikunmu. Kare rayukanmu da iyalanmu da abokanmu da abokan aikinmu ya rataya ne a kanmu.


21. Kamar yadda muka fito da dabarun kare raykanmu daga kamuwa da Covid-19, ina gayyatarku shiga wani shiri na “FORWARD campaign” wanda ke wayar da kan al’umma game da daukan matakan kare kai da cin abinci mai kara garkuwan jiki  a matsayin riga-kafin kamuwa da kwayar cutar.
22. Ku zo mu kare kawunamu:
a. Sanya takunkumi a waje dole ne
b. Bayar da tazara
c. Zama a gida har sai ya zama dole sannan a fito
d. A kaurace wa manyan tarurruka
e. A rika motsa jiki a gida domin zama cikin koshin lafiya
f. Cin abinci mai kyau yana kara garkuwar jiki.

Na gode muku da sauraro.
Ku zauna a gida, ku rayu, ku kare rayuka
In muka hada kai za mu iya yakar Covid-19

Allah ya yi wa Jihar Kaduna albarka
Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Yi Bitar Dokar Da Ta Sa Na Kulle Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Yi Bitar Dokar Da Ta Sa Na Kulle Reviewed by SAMSONGALAXY.com on 10:43 PM Rating: 5

No comments:

Advertise

ismaeeelkwr. Powered by Blogger.