Saudiyya bata ga watan sallah bah


Gwamnatin Saudiyya ta ce sai ranar Lahadi za a gudanar da Idin Salla karama sakamakon rashin ganin jaririn watan Shawwal a ranar Juma'a.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shafin masallacin Harami na Makka da Madinah ya wallafa a shafinsa na Twitter, inda ya ce ba a ga jaririn watan Shawwal ba a yammacin ranar Juma'a bayan duban tsanaki.
Ana dai fara duban watan Shawwal ne a yayin da watan Azumin Ramadana ke cika 29 galibi, a wasu lokutan kuma idan ya kai kwana 30.
Wannan na zuwa ne kwana biyu bayan da masana ilimin taurari suka tabbatar da ba za a ga watan Sallar ranar Juma'a ba.
Jaridar Saudi Gazetteta ruwaito hasashen da suka yi na nuna cewa wata zai riga rana faɗuwa ranar Juma'a, saboda haka ranar Idi ita ce Lahadi 24 ga watan Mayu, yayin da za a yi azumi 30
Saudiyya bata ga watan sallah bah Saudiyya bata ga watan sallah bah Reviewed by SAMSONGALAXY.com on 10:22 AM Rating: 5

No comments:

Advertise

ismaeeelkwr. Powered by Blogger.