BURIN YA MACE

🌹🌹🌹 BURIN KOWACCE MACE🌹🌹

🌺Burin kowacce Mace a rayuwarta ba zai wuce samun muji salihi ingantacce wanda zai zama hasken fitilar rayuwata,
To amma me yasa akasarin mata suka kasa cimma wannan manufa ta su? Me yasa wasu matan suke sukar aure musamman a wannan zamanin? Me yasa wasu matan suka cire fatan samun aminci a cikin rayuwar aure? Me yasa wasu matan suka hakura da aure suka gwammace zama nesa da shi?  Me yasa wasu matan suke shan bakar wahala a ciki zamantakyawar aurensu, me yasa wasu matan suke shiga bokaye da malamai a cikin zamantakyawar aurensu?
💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽💃🏽
Koda yake ita mace takan sa rai da samun aminci a yayin da ta zabi wani a matsayin mijin aure, kuma takan so wannan amincin ya tabbata a dukkan tsawon rayuwarta, to amma Maza sun gaza samarwa da matansu wannan amincin, har ma ta kai ga wasu matan kan yi nadamar yin auren,

Mazan wannan zaman basu cancanta suke matan aure ba ko a basu mace su aura ba har sai an tabbatar lafiyar kwakwalwasu daga likita sbd yadda suke lallabawa su aureki sunana miki so da kuluwa a kafin aure amma da zarar an yi aure sai komai ya rikide ya koma rashin mutunci da rashin imani📞 "inji Muhammad sani sarakee
Mai  nazari akan al'amuran yau da kullum

☘🌷☘🌺☘🌱🌹
Wane laifi Mata suka yiwa Maza ne haka? Da suke gallaza musu suke ci musu mutunci alhali Manzon Rahmah(s) bai bar wannan duniyar ba har sai da ya yi wasiya akan kurike matanku da amana😭  amma da yawan mazan yau sun watsar da wannan wasiya,domin yin hakuri da cutarwar matarka wajibi ne domin an cutar da wadanda suka fika daraja mutunci😭

Yawaitar mutuwar aure a yau ba laifin kowa ba ne illa Maza ne ke da laifi, sbd cin zarafin da wasu mazan kan nunawa matan a zamantakyawar aure wlh ko zaman daduro ne suke sai haka, babu tausayi babu kulawa babu kalaman so da kauna,

Akwai Maxan da ciyar da matansu ma ya gagaresu, tufafin sawarsu sai dai su yiwa kansu, babu kula da halin da matansu ke ciki na rashin lafiya ko cikin wata damuwa, tsakaninsu da matansu sai dai in jima'i kawai 🙈a yi ta tara yara babu kulawa bare a basu tarbiya, ta yaya matarka zata kula da yaranka bayan ita ce ya kamata ka kula da ita, ai sai kogi ya koshi sannan zai shiga gonaki, kuma abin da zai baka mamaki ga irin wadannan Mazan suna samu wata dama sai kuma su kara kinkimo wani auren🤔

Sannan akwai wasu mazan da suke da dabi'ar ha'incin matansu, zasu ci za su sha abu mai kyau a waje amma matansu na fama da garaugarau ko ma fara da mai😭  wasu kuwa mazan kan iya kashe matan da ba nasu ba kudin mai nauyi amma suka kashewa matan sunnarsu 'yan kudi kalilin sai an kai ruwa rana😭

 Na taba jin wani yana sukar matarsa sbd rashin tsaftarta🙈 wai shi yasa wasu matan ke burgeshi a titi🤔 sai na tabmaye shi" Shin duk wata kana bata 10,000 na kayan gyaran jiki? Ai suma matan kan titin kudi suke kashewa jikinsu ba hk Allah ya yi su ba, sata matarka zatayi? Abinci mai gina cikima baka damu ka kawo matarka
 ba, tayaya zata burgeka?

Rikon sakainar,,,,,,,da maza ke yiwa matansu shi ne babbar bazarar wannan al'ummar kuma hatta ma masu addinin haka abin yake, saboda haka maza ku ji tsoron Allah akan hakkokin matanku, aure ba dole bane in kasan ba xaka iya rikewa ba to kaita suburbuda azumin Nafila har ka kai ga ka isa, amma ba daidai bane gidanka ya zama kamar gidan kurkuku ga iyalinka ba,🙈 Mata ku kuma ku kara tunani akan mazan aure ku sa Allah a cikin wannan lamarin domin idan kika biyawa son zuciya to mazan yau zasu kaiki kasuwar dana sani su siyar da ke😭 💜❤💛✍✍✍


BURIN YA MACE BURIN YA MACE Reviewed by SAMSONGALAXY.com on 4:14 AM Rating: 5

No comments:

Advertise

ismaeeelkwr. Powered by Blogger.