RAMADAN
CIYAR DA MAI AZUMI, YA FI DAUKAR NAUYIN TAFSIRI A REDIYO.
Ina taya al’ummar Musulmi murnar shigowar watan Ramadan. Ina kuma yin amfani da wannan dama wajen tunatar da al’ummarmu muhimmancin ciyar da mai azumi. Ina so a tuna da mawuyacin halin da al’umma take ciki a wannan zamani. A rika tunawa da cewa akwai iyalai da yawa wadanda ba su da cin abincin buda-baki ballantana na yin sahur.
A maimakon daukar nauyin tafsiran Malamai da ake yi a gidajen rediyoyi da talabijoji, zai fi kyau idan aka karkatar da kudaden wajen samar da abinci ga iyalan da suke cikin halin kaka-nika-yi.
Mu tuna da cewa, akwai lada mai yawa ga wanda ya samawa mai azumi abinda zai yi duda-baki da shi.
قال رسول الله صلى الله عليه وسلم: من فطَّر صائمًا كان له مثل أجره، غير أنه لا ينقص من أجر الصائم شيء
Mu tuna ya zo a Hadisi cewa: Manzon Allah SAW:
كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَجْوَدَ النَّاسِ بِالْخَيْرِ وَكَانَ أَجْوَدَ مَا يَكُونُ فِي شَهْرِ رَمَضَانَ إِنَّ جِبْرِيلَ عَلَيْهِ السَّلَام كَانَ يَلْقَاهُ فِي كُلِّ سَنَةٍ فِي رَمَضَانَ حَتَّى يَنْسَلِخَ فَيَعْرِضُ عَلَيْهِ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ الْقُرْآنَ فَإِذَا لَقِيَهُ جِبْرِيلُ كَانَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَجْوَدَ بِالْخَيْرِ مِنْ الرِّيحِ الْمُرْسَلَةِ
Ba sai mawadata ba. Kowa ya yi yadda zai iya. Komai kankantarsa. Manzon Allah SAW yana cewa:
اتقوا النار ولو بشق تمرة، فمن لم يجد فبكلمة طيبة
Mu yi kokari mu yaki talaucin zuci.

Reviewed by SAMSONGALAXY.com
on
7:20 AM
Rating:
Reviewed by SAMSONGALAXY.com
on
7:20 AM
Rating:

No comments: