Ƴan takarar shugaban ƙasa a Jamhuriyyar Nijar
Ƴan takarar shugaban ƙasa a Jamhuriyyar Nijar
Ya rage kusan watan biyar a gudaanr da babban zaben shugaban kasa na 2020 zagayen farko a jumhuriyar Nijar. Zuwa yanzu 'yan takara 12 ne suka bayyana anniyarsu ta tsayawa zaben shugaban kasar.
Wadannan 'yan takara na dakon kotun tsarin mulki ta kasa ta tantance su domin su tabbatar da 'yan takarar da suka dace shiga zaben na 2020.
Duk da cewa kotun ba ta bude lokacin yakin neman zabe ba,to amma wasu 'yan siyasa sun fantsama yankunan karkara kuma su na ci gaba da gudanar da taruruka da tattaunawa da jama'a.
Daga cikin wadannan 'yan takara da akwai wadanda suka kasance filin zabe a karo na farko, wasu karon su ne na biyu wasu kuma shi ne na farko, abun da ya sa suka kasance sabbin zuwa a wannan dandali ko kuma filin na takara.
MAHAMANE OUSMANE: A wannan zabe na 2020 zai shiga takarar neman shugaban kasa a karo na bakwai tun lokacin da guguwar dimokradiyya ta shiga jumhuriyar Nijar zuwa yanzu.
A wannan karo zai shiga zaben ne a karkashin jam'iyyar ADR HANKURI CANJI da ke da tuta mai launin kore da fari.
Ƴan takarar shugaban ƙasa a Jamhuriyyar Nijar
Reviewed by SAMSONGALAXY.com
on
10:27 AM
Rating:
Reviewed by SAMSONGALAXY.com
on
10:27 AM
Rating:


No comments: