Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ya yanke jiki ya faɗi yayin da ake tsaka da binciken almubazzaranci da ake zargin hukumarsa da yi.


Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ya yanke jiki ya faɗi yayin da ake tsaka da binciken almubazzaranci da ake zargin hukumarsa da yi. 
Lamarin ya faru ne a yau Litinin yayin da Daniel Pondei yake bayar da bayani ga 'Yan Kwamitin Majalisar Tarayya kan Neja Delta game da yadda hukumar ta kashe biliyoyin naira.
Pondei ya kasa numfashi kuma ya ƙame a kan kujerar da yake zaune. A ƙarshe sai fitar da shugaban daga cikin ɗakin taron aka yi. 
Bisa wannan dalili ne shugaban kwamitin ya bayar da sanarwar tafiya hutun minti 30, inda za su ci gaba da ƙarfe 1:35, a cewarsa. 
A ranar Alhamis Mista Pondei ya fice daga zauren binciken ba tare da an kammala ba, sannan ya zargi shugaban kwamitin, Sanata Olubunmi Tunji-Ojo da cin hanci. 
Yayin wani zama da aka yi a majalisar kasa da ke Abuja a baya, shugaban kwamitin da ke binciken, ya bayyana yadda aka raba kudade a ma'aikatar kamar yadda hukumar ta bayyana musu:
  • An bai wa wani ma'aikaci naira miliyan 10 a matsayin "tallafi"
  • Hukumar NDDC ta raba wa wasu ma'aikata biyu naira miliyan 14
  • Ma'aikata uku kuma sun karbi naira miliya biyar-biyar
  • Ma'aikata 148 an ba su naira miliyan uku-uku
  • Ma'aikata 157 sun karbi naira miliyan daya da rabi-rabi
  • Wasu ma'aikatan 497 sun karbi naira miliyan daya kowannensu
  • Ma'aikatan da ba su sami kudi sosai ba su ne masu shara, wadanda aka mika naira 600,000 ga kowannensu, kuma ya ce sun kai su 464
  • NDDC ta raba wa 'ƴan sanda naira miliyan 475 cikin kuɗin "domin su sayi takunkumi da sinadarin tsaftace hannu".
Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ya yanke jiki ya faɗi yayin da ake tsaka da binciken almubazzaranci da ake zargin hukumarsa da yi. Shugaban Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC) ya yanke jiki ya faɗi yayin da ake tsaka da binciken almubazzaranci da ake zargin hukumarsa da yi. Reviewed by SAMSONGALAXY.com on 7:31 AM Rating: 5

1 comment:

Advertise

ismaeeelkwr. Powered by Blogger.