'Yan Kasuwar Sabon Gari ta Kano na zanga-zanga kan rushe musu kwantainoni

'Yan Kasuwar Sabon Gari ta Kano na zanga-zanga kan rushe musu
'Yan Kasuwar Sabon Gari da ke jihar Kano a Najeriya sun yi zanga-zanga bisa rushe musu wuraren sana'a da suka zargi hukumar KAROTA da yi. 
Wasu daga cikin 'yan kasuwar sun shaida wa BBC cewa dakarun hukumar KAROTA sun rushe musu kwantainoni ba tare da ba su isasshiyar sanarwa ba.
Sai dai shugaban hukumar ya faɗa wa BBC cewa sun shafe kusan tsawon shida da yi wa 'yan kasuwar gargaɗi.
Ya ƙara da cewa ba hukumarsa ce ta yi aikin rushe shagunan ba, kwamiti ne da Gwamnatin Kano ta kafa, wanda ya haɗa da jami'an DSS da 'yan sanda da Civil Defence da kuma KAROTA domin kakkaɓe kasuwanci ba bisa ƙa'ida ba a Kano.
'Yan Kasuwar Sabon Gari ta Kano na zanga-zanga kan rushe musu kwantainoni 'Yan Kasuwar Sabon Gari ta Kano na zanga-zanga kan rushe musu kwantainoni Reviewed by SAMSONGALAXY.com on 7:34 AM Rating: 5

No comments:

Advertise

ismaeeelkwr. Powered by Blogger.